An yi holin masu garkuwa da mutane a Kano

Image caption Rundunar 'yan sanda ta ce za ta cigaba da aiki tukuru don kama masu laifi

Rundunar 'yan sandan jihar Kano a arewacin Nigeria, ta yi holin mutane 32 da ake zargin cewa suna cikin masu yin garkuwa da mutane da suka addabi jihar.

Rundunar ta kuma ce ta kwato makamai daga mutanen da ake zargi suna samun mafaka a dajin Falgore, da ya yi iyaka da wasu manyan dazuzzuka a arewacin Nigeria.

Rundunar ta yi holin mutanen ne a wajen wani gagarumin taro da ta kira a ranar Talata.

Wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai, ya aiko mana da karin bayani daga Kano:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti