Kenya za ta rufe sansanonin 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab

Gwamnatin Kenya ta ce ta yi shirin rufe dukkan sansanonin 'yan gudun hijira a kasar zuwa karshen shekaran nan.

Wani minista a fadar shugaban kasar, Joseph Nkaisserry, ya ce za a mayar da fiye da mutane dubu600, wadanda yanzu suke rayuwa a sansanonin, zuwa kasashensu.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar suna zaune a sansanonin ne tsawon shekara 25.

Gwamnatin Kenyan ta ce zaman 'yan gudun hijirar a kasar wata babbar matsala ce ga tattalin arzikinta, kuma akwai barazanar tsaro a tattare da su.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun soki wannan mataki, inda suka ce Kenyan za ta juya baya ne ga mutanen da rayuwarsu ke cikin hatsari.