Za a ƙwace makaman 'yan Biafra

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police website
Image caption Solomon Arase ya ce 'yan Biafra ba sa son zaman lafiya.

Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya ya buƙaci kwamishinonin 'yan sandan jihohin kudu maso gabas da kudu maso kudancin kasar su ƙwace makaman da ke hannun 'yan fafutikar kafa ƙasar Biafra.

Mista Solomon E. Arase, wanda ya bayar da wannan umarni a wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan ƙasar Olabisi Kolawole ta aikewa manema labarai, ya ce matakin ya zama wajibi ganin yadda 'yan Biafra suka far ma 'yan sandan da ke yunƙurin samar da zaman lafiya a yankin.

Babban Sufeton 'yan sandan ya ce hare-haren da 'yan Biafra suka kai wa 'yan sandan sun nuna cewa ba sa ƙaunar zaman lafiya.

Ya ƙara da cewa rundunar za ta ci gaba da yin bakin ƙoƙarinta domin ganin ta samar da tsaro a Najeriya.

A ranar Litinin ne dai masu fafutukar tabbatar da kafuwar Jamhuriyyar Biafran suka yi bikin cika shekara 50 da ayyana Jamhuriyyar ta Biafra.

Sai dai yayin da aka gudanar da bikin cikin lumana a wasu wuraren, a jihar Anambra an yi arangama tsakanin su da jami'an tsaro, inda ake zargin su da kashe wasu 'yan sanda da ma jama'ar gari.