Giwaye na barazanar karewa a Tanzania

A kasar Tanzania, da yiwuwar Giwayen da ke gandun dabbobin Selous su kare nan da shekaru shida masu zuwa, idan aka ci gaba da farautarsu kamar yadda ake yi a halin da ake cike.

Wani rahoton da gidauniyar raya gandun dabbobi ta World Wildlife Fund ta fitar ya bayyana cewa gandun dabbobin Selous, wanda a shekaru 40 din da suka wuce yana da Giwaye sama da 100,000, yanzu ya yi asarar kashi 90 bisa dari na wannan adadi.

Rahoton ya yi zargin cewa matsalar farautar Giwayen ta yi kamari ne sakamakon karuwar bukatar hauren Giwa, musamman ma daga kasar China.

Sabon shugaban kasar Tanzania dai ya yi alawashin yaki da matsalar cin hanci, wadda ita ce ke bude kofa ga masu fataucin hauren Giwayen ta haramtacciyar hanya.