Layin-dogo mafi tsawo a duniya

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption An shafe shekaru 18 ana gina layin-dogon

A kasar Switzerland, a ranar Laraba ne ake bikin bude wani layin-dogon karkashin kasa mafi tsawo a duniya, bayan an shafe shekara 18 da fara gina shi.

Layin-dogon na Gotthard Base, mai tsawon kilomita 57, an gina shi a karkashin tsaunukan Alps, kuma an tsara shi ne da nufin rage cinkoson abin hawa a kan titunan Swiss.

Layin-dogon zai kasance daya daga cikin hanyoyin da ke danganawa da bangaren arewaci da kuma kudancin Turai.

An bayyana hanyar jirgin kasar a matsayin mai kayatarwa, wanda aka kammala a kan kari, kuma a kan kudin da aka kasafta masa.

Wakiliyar BBC ta ce aikin gina layin dogon ya ci dala biliyon 12, kuma yayin aikin an fafe duwatsu, wadanda garin da aka rarake kadai zai kai a gina dalar dutse shida irin ta kasar Masar, don haka mahukuntan Switzerland sun ce aikin ya ci kudinsa.

A watan Disamba mai zuwa ne ake sa ran za a fara harkar kasuwanci ta layin-dogon, jiragen kaya sama da 250, da kuma jiragen Fasinja 65 za su dinga yin jigila a kowace rana.