Shugaban Venezuela ya ɓata da 'yan majalisa

Hakkin mallakar hoto re

Kungiyar hada kan kasashen da ke yankin Amurka za ta yi wani taron gaggawa don tattaunawa a kan rikicin da ya dabaibaye kasar Venezuela, kuma taron ne zai ba da damar dakatar da kasar daga cikin kungiyar.

Shugaban kungiyar, Luis Almagro, ya ce gwamnatin Venezuela na yin zagon-kasa ga demokuradiyya, tare da daure masu adawa da ita ba gaira ba dalili.

Sai dai shugaban kasar, Nicolas Maduro ya mai da martani a kuntume, yana zargin Luis Almagro da cewa karen farautar Amurka ne.

Kazalika shugaba Maduro ya yi barazanar gufanar da 'yan majalisar dokokin kasar gaban Alkali dangane da bukatar da suka gabatar ga Kungiyar hada kan kasashen da ke yankin Amurka cewa ta sa baki a cikin rikicin Venezuela.

Ya ce ya yanke shawara zai sa ma'aikatar harkokin waje da Ministan Shara'a su shigar da kara suna tuhumar majalisar dokoki da yin zagon-kasa ga ikon shugaban kasa.

Tattalin arzikin Venezuela dai ya durkushe, lamarin da ya haddasa karancin abubuwan more rayuwa, tare da haddasa rikici tsakanin shugaban kasa mai ra'ayin gurguzu da kuma 'yan adawa.