Za a yi bincike kan kisan goggon biri

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Butum-butumin goggon biri Harambe kenan a gidan namun daji

'Yan sanda a Amurka sun ce za su mayar da akalar tuhumarsu kan iyayen wani yaro dan shekara uku da ya shiga kejin wani katon goggon biri a gidan namun daji na Cincinnati, al'amarin da ya kai ga harbe birin.

Mai shigar da kara na gundumar, Hamilon Joseph Deters, ya ce 'yan sanda za su bai wa ofishinsu hadin kai domin gabatar da tuhumar aikata mugun laifi.

Hukumar gidan namun dajin ta ce ba ta da wani zabi ne sai na kashe goggon birin, ta kuma kare matakan kariya da ta dauka a kewayen kejinsa.

Sai dai masu fafutukar kare hakkin namun daji sun yi zargi hukumar gidan ajiye namun dajin da aikata ba daidai ba.

'Yan sanda sun ce binciken da za su yi kan al'amarin zai yi duba ne kan sakacin iyayen yaron amma ba kan yadda gidan namun dajin ke gudanar da ayyukansa ba.

'Tsaka mai wuya'
Hakkin mallakar hoto
Image caption Yadda birin ya dinga jan yaron cikin ruwa

A ranar Asabar ne yaron mai shekara uku ya fada kejin goggon birin mai shekara 17 mai suna Harambe.

Wani bidiyo da aka dauka ya nuna yadda birin ke jan yaron cikin ruwa.

Da fari dai an ga kamar birin yana kare yaron ne tare da kula da shi, amma daga bisani sai ya fara fisgarsa cikin ruwan da karfi, sakamakon ihun da ya ji wadanda ke kallon abin da ke faruwa suke yi.

'Ceton rai'

Ganin haka ne ya sa masu kula da gidan namun daji daukar matakin harbe birin har lahira saboda tsoron kada ya kashe yaron ko yi masa illa.

Sai dai wannan abu ya jawo lugudan labba ba kadan ba har a shafukan sada zumunta da muhawara a sassa daban-daban na duniya.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Zanga-zangar da wasu suka yi don nuna fushi da kashe Harambe

Wasu da dama na ganin bai kamata a kashe tsohon birin mai nauyin kilo 400 ba, wanda kuma ire-irensa ke barazanar bacewa a doron kasa, saboda ceto ran yaro.

Yayin da wasu ke ganin rayuwar dan adam ta fi gaban ta dabbobi nesa ba kusa ba.

Rahotanni sun ce goggon birin yana da tsananin karfin da zai iya fasa kwakwa da hannunsa.