An kai kayan agaji Darayya a karon farko

Image caption Motar kai kayan agaji ta Majalisar Dinkin Duniya

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce ayarin motocin kayan agaji ya isa garin Darayya da aka yi wa kawanya a kusa da birnin Damascus na Syria.

Kungiyar ta ce wannan shine karo na farko da aka kai irin wannan agaji tun watan Nuwambar shekarar 2012.

Jami'an bayar da agaji na Majalisar Dinkin Duniya sun ce al'ummar garin na cikin matukar bukatar abinci da tsaftataccen ruwa sha da magunguna.

Da safiyar Laraba ne aka fara aiki da wata yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa'o'i 48 a garin, wanda ke kudu da babban birnin Syria.

Hukumar bayar da agajin jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce cikin kayayyakin da aka kai garin, akwai magunguna da madara ta yara da sauran su.

Shi ma garin Muadhamiya da ke arewa maso yammacin Darayya, an kai masa kayan abinci da garin alkama, bayan wata daya da kai irin wadannan kayan a garin.

A watan Afrilu ne, Majalisar Dinkin Duniya ta ce a kalla mutane dubu hudu ne dakarun gwamnati suka yi wa kawanya a garin Darayya.