Fasfo: Tsoffin gwamnoni na 'tsaka mai wuya'

Wasu tsofaffin gwamnoni da tsaffin ministoci da 'yan majalisar dokoki a Nigeria na tsaka mai wuya bayan da hukumar shige da ficen kasar ta ce dole ne su dawo da fasfunan diflomasiyya.

Shugaban Hukumar shige da ficen ta Nigeria, Muhammad Babandede, a tattaunawar shi da Ibrahim Mijinyawa, ya ce abin takaici ne yadda irin wadannan mutane suka ki mayar da fasfunan diflomasiyyar bayan sun sauka daga mukamansu.

Ga karin bayanin da shugaban hukumar shige da ficen ya yi kan umurnin kama wadannan mutane da suka ki mayar da fasfunan na su:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti