An kashe wanda ya kitsa harin Garissa

Hakkin mallakar hoto Kenya Interior Ministry
Image caption Mohamed Kuno

Hukumomi a Somalia sun ce an kashe mutumin da ya jagoranci harin da aka kaddamar a jami'ar Garissa da ke Kenya a shekarar 2015.

A baya dama, gwamnatin Kenya ta sanar da sunan Mohamed Kuno a matsayin wanda ya kitsa harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 148.

Dakarun soji na yankin dake aiki a Somalia sun ce Kuno, daya ne daga cikin mutane 16 da aka kashe lokacin wani samame a Kismayo, dake kudancin kasar.

Rahotanni sun ce hudu daga cikin wadanda aka kashe manyan mayakan kungiyar al-Shabab ne.

A ranar Laraba ne Ministan Tsaro na yankin Jubaland a Somalia Abdirashid Janan, ya tabbatar da labarin a wurin wani taron manema labarai.

Bayan harin na Garissa, gwamnatin Kenya ta sanya ladan $215,000 ga duk wanda ya taimaka aka kama Kuno.

Kuno dan Kenya ne wanda ke da asali a Somalia, kuma a baya shugaban wata makarantar Islamiyya a Garissa har zuwa shekara ta 2007.

Daga nan ne ya tsallaka kan iyaka zuwa Somalia domin shiga kungiyar mayakan Islama ta Union of Islamic Courts (UIC), wacce a wani lokaci a baya take rike da ikon mafi yawancin kasar.

Bayan da kungiyar ta UIC ta rushe ne kuma ya shiga kungiyar Hizbul Islam, wacce ta hade kungiyar al-Shabab a shekara ta 2010.