An kona malama don ta ki aure a Pakistan

Image caption Ana yawan kai wa mata hare-hare saboda kin baiko

Wata malamar makaranta ta mutu bayan da wasu mutane suka cinna mata wuta saboda ta ki yarda da baikon da aka yi mata a Pakistan.

Iyalan matar mai suna Maria, mai kimanin shekara 20, sun ce mutanen sun kai mata hari ne bayan da ta ki yarda da baikon da aka yi mata.

'Yan sanda sun shaida wa BBC cewa wasu mutane ne suka shiga gidanta suka yi mata duka kana suka watsa mata man fetur kafin daga bisani suka cinna mata wuta.

Masu fafutuka sun ce hare-haren da ake kai wa matan da suke kin yarda da baikon da ake yi musu ya zama ruwan dare a Pakistan.

Karin bayani