An kai hari kan wani otal a Somalia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ko a watan Janairu ma an kai wani hari a otal a Burkina Faso

Rahotanni daga Somaliya na cewa 'yan bindiga sun dirar wa wani otal da ke tsakiyar babban birnin kasar, Mogadishu, sun kuma kashe mutane 10.

Wadansu da suka shaida faruwar lamarin sun kutsa kai cikin otal din Ambassador da ke kan titin Makka al-Mukarrama, bayan da suka dana wa wata mota da ke kofar shiga otal din bam.

'Yan sanda sun ce dakarun tsaro sun shiga cikin otal din wanda matattara ce ta 'yan siyasa da jami'an gwamnati, domin fafatawa da 'yan bindigar.

Tuni kungiyar Al-Shabab ta dauki alhakin kai harin.

Karin bayani