Me ya hana Buhari zuwa taron share Ogoni?

Image caption Farfesa Yemi Osinbajo ne zai wakilci Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya soke ziyarar da zai kai Naija Delta domin kaddamar da shirin share man da ke malala a yankin.

Babu wata hujja da aka bayar ta soke ziyarar, sai dai wasu majiyoyi na cewa hare-haren da masu tayar da kayar baya ke kaiwa ne suka hana shi zuwa.

A baya bayan nan 'yan bindiga na kungiyar Niger Delta Avengers sun rika fasa bututan man fetur, yayin da suke ci gaba da yin barazanar kaddamar da hare-hare.

Mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ne ya wakilci Mr Buhari a wurin taron.

A watan jiya ma, Shugaba Buhari ya soke ziyarar da aka tsara zai kai jihar Lagos, a Kudu maso Yammacin kasar.

A lokacin, wani kakakin shugaban kasar ya ce an soke ziyarar ne saboda aikace-aikace sun yi masa yawa.

Shugaba Buhari ya sha alwashin kawo karshen matsalolin da suka addabi yankin na Naija Delta.

Haruna Shehu Tangaza, daga Aso Villa, Abuja

Kawo yanzu babu wani bayani a hukumance daga kowacce kafa a fadar shugaban kasa kan rashin zuwan shugaban Buhari wajen kaddamar da aikin share malalar mai a yankin Ogoni.

Sai dai wasu majiyoyi da ba na hukuma ba na jin cewa, rashin halartar shugaban kasar dalilai ne na tsaro.

Rahotanni a kafafen sada zumunta sun ce kungiyar Niger Delta Avengers ta sha alwashin kai hare-hare a yayin ziyarar.

Shugaba Buhari ya kasance a ofishinsa a ranar Alhamis din domin ci gaba da tafiyar da al'amuran kasa har ma ya fito sallar Azahar.

Hakkin mallakar hoto NGR
Image caption Rashin zuwa Ogoni bai hana Buhari aiki a ofishinsa ba a ranar Alhamis

Halartar shugaba Buhari wannan taro yana da matukar muhimmanci ta fuskar siyasa, ganin cewa aiki ne da gwamnatocin baya suka kasa yi, amma shi ya kuduri aniyar aiwatarwa.

Baya ga haka, Naija Delta yanki ne da jam'iyyar adawa ke da karfin gaske kuma yanki ne da al'ummarsa ke guna-gunin cewa ba a yi musu adalci wajen tafiyar da harkokin kasa.

Sai dai soke ziyarar za ta iya zamowa koma-baya ga yunkurin da shugaban ke yi na janyo 'yan yankin na Naija Delta a jikinsa.