'A biya kamfanonin jiragen sama na waje kudadensu'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Kungiyar masu zirga-zirgar jiragen sama ta duniya, IATA, ta bukaci Najeriya ta biya kamfanonin jirage na kasashen waje kudadensu na tikiti ko ta fuskanci fushin kungiyar.

Kudaden dai sun kai dala miliyan 591.

Bisa al'ada dai babban bankin Najeriya ne yake juya wa kamfanonin kudadensu na ciniki daga Naira zuwa Dalar Amurka.

Sai dai a yanzu kasar na fuskantar matsalar hauhawar farashin kudaden waje.

A makon jiya ne kamfanin jiragen sama na kasar Jamus, Lufthansa ya dakatar da zirga-zirga zuwa Venezuela, saboda rashin biyansa kudaden tikitinsa.

A wata sanarwa da kungiyar ta IATA fitar bayan taronta na shekara-shekara da aka gudanar a Dublin, ta ce hana kamfanonin jirage kudadensu na taimakawa wajen karya tattalin arzikin kamfanonin.