Messi zai bayar da shaida a kotu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana zargin Messi da zillewa biyan haraji

Dan kwallon tawagar Argentina, Lionel Messi, zai bayar da shaida kan zargin kaucewa biyan haraji da ake tuhumarsa.

Ana zargin Messi da mahaifinsa mai kula da harkokin kudin dan kwallon da kin biyan haraji ga mahukuntan Spaniya da suka kai sama da fan miliyan uku daga tsakanin shekarar 2007 zuwa 2009.

Mahukuntan Spaniya sun yi zargin cewar an yi amfani da wasu asusun ajiya a Belize da Uruguay domin binne kudaden shiga da dan kwallon ke samu a fannin tallace-tallace.

Hukumar karbar harajin ta Spaniya na bukatar hukuncin tara mai tsanani da zaman jarun, sai dai kuma wadanda ake zargin sun musunta aikata ba daidai ba.

Tun a ranar Talata aka fara sauraren karar, wadda ake sa ran jin bahasi na karshe a ranar Alhamis, yayin da ake sa ran yanke hukunci a mako mai zuwa.

A dalilin karar da ake saurara ne ya sa Messi bai halarci shirye-shiryen da Argentina ke yi domin tunkarar gasar Copa America da za a fara a ranar Juma’a ba.