NDA ta kai hari kan bututun mai na Shell

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption NDA ta zafafa kai hare-hare kan bututan man Najeriya a kwanakin nan.

Kungiyar masu tayar da kayar baya ta Niger Delta Avengers (NDA), ta ce dakarunta sun kai hari kan bututun mai na Forcados mallakin kamfanin mai na Shell.

Wannan lamari na zuwa ne kwana guda bayan da gwamnati ta kaddamar da gagarumin shirin share dagolon man da yaya lalata yankin Ogoni na jihar Rivers.

NDA ta sha alwashin yin zagon kasa ga ayyukan hakar mai a yankin.

Masu sharhi na ganin cewa kungiyar na son ganin al'ummar yankin sun samu karin iko ga arzikin man da ake hakowa a garuruwansu.

A wani lamarin na daban kuma, rundunar sojin Nigeria ta ce 'yan bindiga sun kashe mutane takwas a garin Warri na jihar Delta.

Sai dai NDA ta ce ba ita ce ta kai harin ba.

Hare-haren da ake kaiwa a yankin Naija Delta a 'yan kwanakin nan sun sanya adadin man da Nigeria ke fitarwa kasuwannin duniya ya ragu.