Su waye 'yan kungiyar Niger Delta Avengers?

Niger Delta Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tsagerun Naija Delta sun dade suna kai hari kan kamfanonin kasashen waje

Kungiyar Niger Delta Avengers (NDA), ita ce kungiyar 'yan bindiga da ta bullo a baya-bayan nan a yankin Niger Delta da ke kudancin Najeriya.

Wannan kungiyar dai tana kai hare-hare ne kan kamfanonin hakar mai da suke yankin, kamar su Shell da Chevron da Agip da sauransu, inda suke fasa bututan man da ake amfani da su.

A watan Afrilun 2016 ne, kungiyar ta fitar da sanarwa ta farko a shafinta na intanet, inda ta rubuta kamar haka, ''Mu kungiya ce ta masu ilimi wadanda suka san duniya sosai, masu kuma burin ganin sun yi fafutukar samo wa yankin Naija Delta mafita irin wacce ba a taba gani ba a kasar.''

Sanarwar ta kara da cewa, ''Muna da dukkan hanyoyin da za mu bi domin cimma burinmu.''

'Waye jagoran kungiyar?'

A baya can akwai kungiyoyin 'yan bindiga da dama a yankin Naija Delta da ke kai hare-hare kan kamfanonin mai da kuma garkuwa da mutane, saboda abin da suka kira fafutukar neman 'yanci.

Sun ce suna adawa ne da abin da suka kira 'Rijiya ta bayar da ruwa amma guga ya hana,' ta yadda ga arziki a kasarsu amma ba sa cin moriyarsa sai dai wasu daban su ci, su kuma suna cikin wahala.

A shekarar 2008 ne shugaban Najeriya Umar Musa 'Yar adua ya yi wa kungiyoyin 'yan bindigar afuwa da kuma sasantawa da su. Har ma aka ware makudan kudade don tallafa musu.

Zai yi wuya farat daya a iya cewa ga shugaban wannan kungiya ta NDA ko kuma mambobinta. Sai dai hoton da ke kan shafinsu na Twitter na kungiyar MEND ce wadda tana daya daga cikin kungiyoyin 'yan bindiga da suka yi tasiri a baya a yankin Naija Delta.

Amma al'ummar yankin sun yi amannar cewa mambobin kungiyar NDA yawancinsu 'yan tsofaffin kungiyoyin 'yan bindigar yankin ne kamar MEND, wadda Henry Okah ke shugabanta, ko kuma 'yan kungiyar Niger Delta People's Salvation Front ta Mujahideen Asari Dokubo.

Mutane da dama na cewa 'yan bindigar NDA mabiyan tsofaffin tsagerun yankin Naija Delta ne kamar su Government Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo.

Duk da cewa Tompolo ya nisanta kansa da kungiyar, amma babu wani daga cikin tsofaffin jagororin kungiyoyin 'yan bindigar da ya tofa tasa kan batun.

Wasu kuwa na ganin sabbin 'yan bindigar wasu tsageru ne da ke son jan hankalin duniya ganin cewa yanzu dan uwansu tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, ba shi ne a ragamar mulkin kasar ba.

Har yanzu dai ba wanda zai iya bugar kirji ya fadi jagoran kungiyar NDA, duk da cewa Kanal Mudoch Agbinibo shi ne wanda yake sanya hannu kan duk wata sanarwa da kungiyar ke fitarwa.

Ko ma dai wanne irin tunani mutane ke yi game da kungiyar, ya bayyana karara cewa ana shirya ayyukan da ta ke yi a yankin Naija Delta da kyua cikin taka tsan-tsan da kwarewa.

'Tabarbarewar tattalin arziki'
Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yankin Naija Delta na da arzikin man da Najeriya ta dogara da shi

Kamar yadda kungiyar NDA ta sha alwashin kai hare-haren da za su shafi harkar hakar mai a yankin Naija Delta, to ba su yi kasa a gwiwa ba wajen cimma burinsu.

NDA ta kai hare-hare da dama kan bututan mai inda aka samu raguwar man da ake haka sosai a yankin, kuma kaso mafi yawa na tattalin arzikin Najeriya ya ta'allaka ne a kan wannan mai.

An ambato ministar kudi ta Najeriya Kemi Adeosun a gidan talbijin na kasar tana cewa, ''Sabbin hare-haren da 'yan bindiga suke kai wa kan kamfanonin hakar mai a yankin Naija Delta na matukar shafar samar da man da kasa ke yi.''

Dama dai kungiyar NDA ta bayyana manufofinta na abin da take son cimmawa. Ta ce: ''Burinmu shine mu durkusar da tattalin arzikin Najeriya.''

Bayan ta kaddamar da abin da ta kira "Operation Red Economy" a watan Fabrairu, ta fasa wani bututun mai da ke karskashin ruwa, abin da ya tursasa kamfanin Shell rufe tasharsa inda a duk rana yake samar da gangar danyen mai 250,000.

'Barna'
Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kamfanin Shell na daga cikin kamfanonin da ke hakar mai a yankin Naija Delta

A watan da ya gabata ne Shell ya sanar da dakatar da ayyukansa da suka hada da na yarjejeniyoyin fitar da danyen mai daga kasar.

Kwanaki kadan bayan nan kamfanin Chevron ma ya rufe sakamakon harin da NDA ta kai masa.

Kungiyar NDA ta sake kai hari tashar hako mai ta Chevron daf da ziyarar mataimakin shugaban Najeriya zuwa yankin Ogoni don kaddamar da share malalar mai.

Wadannan hare-hare sun yi matukar tasiri ga kudin shigar Najeriya da fitar da mai.

A takaice dai fitar da man da kasar ke yi ya ragu zuwa ganga miliyan 1.65 a duk rana maimakon miliyan 2.2 da ake samarwa a baya.