'Hare-haren ta'addanci sun ragu a 2015'

Ma'aikatar hulɗa da ƙasashen wajen Amurka ta ce an samu raguwar hare-haren ta'addanci a faɗin duniya cikin shekara ta 2015.

Alƙaluman da aka fitar sun danganta raguwar hare-haren ga raguwar hare-haren ta'addanci a Iraki, da Pakistan, da kuma Nigeria, wanɗanda su ne ƙasashen da suka fi fama da ta'addanci.

Sauran ƙasashen da suke fama da ta'addanci sune, India da kuma Afghanistan.

Rahoton ya kuma ce duk da raguwar hare-haren ta'addanci ƙungiyar IS tana ci gaba da kasancewa babbar barazana.

Dakta Abdullahi Wase wani mai sharhi ne kan al'amuran tsaro a Najeriya kuma Isa Sanusi ya tambaye shi ko ya yi mamaki da wannan rahoton:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ko da ƙungiyar Boko Haram ta taɓa ayyana haɗewa da ƙungiyar IS dake da ƙarfi a Syria da Iraki.

A wani rahoto mai alaƙa da wannan majalisar ɗinkin duniya ta ce, ƙungiyar IS tana ƙarfafa kai hare-hare akan wurare na suka shafi ƙasa-da-ƙasa.