Donald Trump ba shi da manufa — Clinton

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Da alama Trump da Hillary ne za su fafata a zaben shugabancin Amurka.

Matar da ke son yi wa Democrat takarar shugabancin Amurka Hillary Clinton ta bayyana abokin hamayyarta na jam'iyyar Republican Donald Trump a matsayin "mutumin da kwata-kwata ba a fahimtarsa".

Clinton ta ce bai kamata Mista Trump ya zama shugaban kasa ba, tana mai cewa idan aka zabe shi za a yi kuskuren da ba a taba yi ba a Amurka.

Sai dai Mista Trump ya yi mata raddi, yana mai cewa Mrs Clinton "ba ta da kima da martaba saboda ta sha yin kuskure a mukaman da ta rike".

Masu goyon bayan Mista Trump da masu hamayya da shi sun arangama a kusa da wajen da yake yakin neman zabe a San Jose na jihar California.