Ana alhinin mutanen da suka mutu a Ghana

Al'umar kasar Ghana tana yin jimami da addu'oin cika shekara daya da aukuwar wata mummunar ambaliyar ruwa da tashin gobara a wani gidan mai da ke birnin Accra, lamarin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 153.

Ambaliyar ruwan, wacce ta hadu da man fetur din da ya kwaranya ranar uku ga watan Yunin shekarar 2015, ta kara munana lamarin.

Har yanzu dai ba a kai ga gano wasu daga cikin gawarwakin mutanen da suka mutu ba.

Shugaba John Mahama, wanda ke halartar wajen addu'o'in, ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa hukumomi za su yi bakin kokarinsu na ganin irin hakan bai sake aukuwa ba.

Kazalika shafukan sada zumunta da muhawara sun rika amfani da wani maudu'i mai suna #RememberJune3, wato tunawa da bala'in da ya faru ranar uku ga watan Yuni, domin bayyana jimaninsu.