Nigeria ta sanar da kuɗin Hajjin bana

Hakkin mallakar hoto AFP

Hukumar aikin Hajji ta Nigeria ta sanar da kuɗin aikin Hajji da maniyyatan bana zasu biya.

Hukumar ta bakin kakakinta, Alhaji Uba Mana ta ce, bana kuɗin guzuri mafi ƙaranci shi ne na ƙaramar kujera shi ne, dala 750 ga maniyyan jihohin arewacin Nigeria, kuma ƙudin aikin Hajjin shi ne

N998, 248.92, yayin da su kuma maniyyatan kudancin Nigeria zasu biya N1,008,197.42.

Kujera tsaka-tsaki kuma zata kama N1,047,498.92, da kuɗin guzuri dala $1000 ga 'yan arewacin Nigeria, amma maniyya daga kudu zasu biya N1,057,447.42.

Sanarwar ta kuma ce, maniyyan da suke son riƙe guzuri mafi yawa na dala $1,500 zasu biya N1,145,998.92.

Hukumar aikin Hajjin ta Nigeria ta kuma buƙaci hukumomin alhazai su hanzarta karɓar kudaden aikin hajjin domin shirin aikin na bana ya kammala akan lokaci.