Japan: An gano yaron da ya ɓata a tsaunuka

Hakkin mallakar hoto AFP

A Japan, an gono yaron nan ɗan shekaru bakwai Yamato Tanooka, kwanaki bakwai bayan mahaifansa sun baro shi a wani yanki mai tsaunuka dake arewacin kasar.

An gano yaron ne a kusa da wani sansanin sojoji da ke da nisan kilomita huɗu daga inda mahaifansa suka yi watsi da shi.

A baya dai iyayen yaron cewa suka yi ya bata ne a lokacin da yake tsinkar ganyaye.

Amma daga bisani suka ce sun bar shi ne na dan wani lokaci a kan hanyar wani tsauni a matsayin wani horo saboda rashin ji.

Jim kadan bayan da suka dawo daukarsa sai suke neme shi ko kasa ko sama.

An kuma gano Yamato kafin karfe takwas na safiyar Jumma'a wato karfe 11 agogon GMT na ranar Alhamis aka gano shi a cikin rumfar.

Nan da nan kuma aka garzaya da shi zuwa asibiti a cikin jirgin daukar marasa lafiya mai saukar angulu don duba lafiyarsa.