'Yan Kannywood na baje-koli a shafukan zumunta

Samuwar shafukan sada zumunta da muhawara na zamani irin su Facebook, da Twitter da Instagram, ta kawo sauye-sauye a fannoni da dama na rayuwar dan adam.

Shafukan sun kawo sauyi a yadda ake kasuwanci da neman ilimi da samun labarai da ma 'tsegumi'.

Hakan ne ya sa 'yan wasan kwaikwayon Hausa, wadanda aka fi sani da 'yan Kannywood, suka riki wadannan shafuka wajen ganawa da masoyansu.

Binciken da na yi ya nuna cewa akasarin 'yan wasan Kannywood na yin amfani da shafin Instagram, kuma hakan ba ya rasa nasaba da kasancewar shafin wani dandali da ake wallafa hotuna da bidiyo, wanda dama shi ne burin masu sana'ar fim.

Sai dai baya ga Instagram, wasun su suna amfani da Twitter da kuma Facebook, ko da ya ke bincike ya nuna cewa 'yan Kannywood din suna 'tsoron' Facebook ne saboda ana yawaita samun masu yi musu sojan-gona.

Mun yi nazari kan yadda wasu fitattun 'yan fim ke baje-kolinsu a wadannan shafuka:

Hakkin mallakar hoto Ali Nuhu
Image caption Ali Nuhu ya dade yana jan zarensa a Kannywood

Ali Nuhu

Ali Nuhu, ko "Sarki", kamar yadda aka fi sanin sa a Kannywood, shi ne mutumin da ya fi mabiya a Facebook, inda yake da mabiya sama da miliyan daya.

Baya ga Facebook, fitaccen dan wasan kwaikwayon yana da mabiya fiye da 200,000 a Instagram, yayin da yake da mabiya sama da 91,000 a Twitter.

Yawanci dai yana amfani da shafukan ne wajen aikewa da hotuna da bidiyo da kuma labaran irin fina-finan da yake fitowa.

Hadiza Gabon

Hakkin mallakar hoto Hadiza Gabon
Image caption Hadiza Gabon tana yawan murmushi

Za a iya cewa babu wani dan wasan Kannywood da ya fi wannan kyakkyawar 'yar wasa yawan mabiya a shafin Instagram. Tana da mabiya sama da 253,000.

Masu kula da irin mu'amalar da 'yan Kannywood ke yi na ganin hakan na da alaka da yawan sanya hotuna da bidiyon da take yi wadanda ke nuna ta cikin annashuwa da yawaita murmushi.

Kazalika, 'Indon Kauye', kamar yadda ake kiranta a wani fim din barkwanci da ta yi, tana yawan "gaishe da masu bibiyar" shafukanta da kuma gode musu.

Rahama Sadau

Hakkin mallakar hoto Rahama Sadau
Image caption Ana yi wa Rahama lakabi da Sizzling Siren, watau "tauraruwa mai walkiya"

Wannan fitacciyar 'yar wasan ta Kannywood, wacce kuma ta fara fitowa a fina-finan kudancin Najeriya, Nollywood, tana da mabiya sama da 249,000 a Instagram, yayin da fiye da mutum 47,000 ke bin ta a Twitter.

Rahama, wacce ake yi wa lakabi da Sizzling Siren, watau "Tauraruwa mai Walkiya", ta fara fitowa a wani fim mai suna 'Gani Ga Wane', kuma tun daga lokacin tauraruwarta ke haskakawa a Kannywood, inda yanzu take cikin manyan 'yan fim din da ake ji da su.

Adam A. Zango

Hakkin mallakar hoto Adam A Zango
Image caption Adam A. Zango ya taba bayyana kansa a matsayin "dankali sha kushe"

Hausawa na cewa Yarima Gatan Sarki. Watakila hakan ne ya sa "Prince Zango", wanda ke taka rawa daban-daban a masana'antar fina-finan Hausa, ya dade yana jan zarensa.

Zango dai mawaki ne, haka kuma yana bayar da umarni, kana yana fitowa a matsayin jarumi. Wannan basira da Allah ya yi masa ta sa yana da mabiya sosai a shafukansa na sada zumunta.

A Instagram kadai, yana da mabiya 147,000, yayin da yake da mabiya kusan 7,000 a Twitter.

Nafisa Abdullahi

Hakkin mallakar hoto Maikatanga
Image caption Nafisa Abdullahi ce jarumar jarumai, yayin da Saddiq Sani Saddiq ya lashe kyautar jarumin jarumai a bikin Kannywood na shekarar 2015.

Tun lokacin da ta fara fitowa a fim din 'Sai Wata Rana', Nafisa Abdullahi ta ja hankulan masu kallon fina-finan Kanyywood. Salonta na iya yin kuka a fim na daukar hankalin masu kallo.

Nafisa tana da mabiya sama da 189,000 a shafinta na Instagram, yayin da take da mabiya kusan 42,000 a Twitter.

Saddiq Sani Saddiq

Ɗan Marayan Zaki, shi ne sunan da wadansu ke kiransa. Sau biyu a jere, Saddiq yana lashe kyautar Jarumin-Jarumai ta Kannywood.

Yana fitowa a manyan fina-finai, sannan ya iya amfani da kalmomi wajen isar da sakonsa. Fim dinsa na baya-bayan nan da ya fi jan hankalin masu kallo shi ne 'Mati Da Lado'.

Saddiq yana da mabiya a shafin Instagram sama da 111,000.

Maryam Booth

Hakkin mallakar hoto maryam booth
Image caption Maryam Booth ta kware wajen iya kwalliya

Wannan kyakkyawar 'yar Kannywood din tana da mabiya sama da 192,000 a Instagram. Tana yawaita sanya hotunanta cikin kayan kawa da tallata wasu hajojinta.

Fati Washa

Hakkin mallakar hoto fati washa
Image caption Fati Washa tana fitowa a manyan fina-finai

Fati Washa na sahun farko na 'yan matan da ake ji da su a Kannywood. Ta fito a fina-finai masu dimbin yawa, inda akasari take fitowa a matsayin jaruma.

Tana da mabiya fiye da 184,000 a Instagram.

Nuhu Abdullahi

Hakkin mallakar hoto NUHU ABDULLAHI
Image caption Nuhu Abdullahi ya gamu da fushin hukumar tace fina-finan Kano

Wannan matashin jarumin yana fitowa a manyan fina-finai. Sai dai wani fim da ya dauki nauyinsa, 'Ana Wata Ga Wata' ya janyo masa fushin hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano, wacce ta gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin fitar da fim din, wanda ta bayyana da cewa yana kunshe da kalamai na rashin sanin ya kamata.

Nuhu Abdullahi yana da mabiya 64,000 a shafin Instagram.

Aminu Saira

Hakkin mallakar hoto AMINU SAIRA
Image caption Aminu Saira ya shahara wajen yin manyan fina-finai

Malam Aminu Saira, kamar yadda aka fi sanin sa, fitaccen mai hada fina-finan Kannywood ne, kuma ya taba shaida wa BBC cewa babu abin da yake burge shi kamar hada fim din da zai ilimantar da mutane.

Aminu Saira ya hada fina-finai da dama cikin su har da 'Daga Ni Sai Ke', wanda yar burge dimbin masu kallo. Yana da mabiya 94,000 a Instagram.

Falalu Dorayi

Hakkin mallakar hoto FALALU DORAYI
Image caption Ana yi wa Falalu Dorayi lakabi da "Dattijon Industry"

Ana yi masa lakabi da "Dattijon Industry" saboda halayensa na dattaku da tsayawa kan gaskiya. Falalu Dorayi ya yi fice wajen bayar da umarni, sannan yana fitowa a matsayin jarumi.

Ya taba shaida wa BBC cewa babban abin alfaharinsa shi ne "yadda wani ya Musulunta ta hanyar fim din da na hada".

Masu bibiyar masana'antar Kannywood sun ce Falalu Dorayi ba ya wasa da aiki da kuma biyan mutum idan ya kammala aikinsa. Yana da mabiya sama da 62,000 a shafin Instagram.

Aisha Tsamiya

Hakkin mallakar hoto AISHA TSAMIYA
Image caption Aisha Tsamiya ta yi suna sosai saboda rawar da ta taka a fim din "Dakin Amarya"

Fim din da ya fito da ita shi ne 'Dakin Amarya', kuma tun daga lokacin take fitowa a manyan fina-finai.

Ta iya kalamai na kwantar da hankalin 'miji' a dukkan fim din da ta fito, sannan ta gwanance wajen taka duk rawar da mai ba da umarni ya ce ta taka. Tana da mabiya 145,000 a Instagram.