'An gano maganin cutar tumatir'

Tumatir
Image caption Manoman tumatir sun yi asarar miliyoyin daloli

Wata cibiyar bincike a Najeriya ta ce ta gano wani magani da zai iya kashe kwarin tumatir wadanda suke kashe amfanin da aka noma.

A watan da ya gabata ne jami'ai a Najeriya suka ce wani kwaro wanda ake kira moth ya lalata kashi 80 na gonakin tumatir da ke jihar Kaduna.

Cibiliyar Kimiyyar Hada Sinadarai ta kasa da ke Zaria ta ce maganin zai taimaka sosai wurin kawo karshen annobar, wacce ta haddasa wa manoma asarar miliyoyin daloli a arewacin kasar.

"Mun gano cewa daya daga cikin sanadaren da muke amfani da su wurin hada taki ne zai taimaka wurin maganin wannan cuta," a cewar shugaban hukumar Diya'udden Bashir Hassan.

Farashin tumatir ya yi tashin gwauron zabi daga dala daya da 'yan kwabbai a watannin uku da suka wuce zuwa sama da dala 40.

Haka kuma ana matukar karancinsa a dukkan fadin kasar, inda ya gagari mafi yawan magidanta.

Lamarin ya sa gwamnatin Kaduna kafa dokar tabaci kan tumatir.

A yanzu mafi yawan jama'a na dogaro ne kan tumatirin gwangwani da ake shigowa da shi daga kasashen waje.