Za a yi jana'izar Muhammad Ali ranar Juma'a

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Iyalan marigayi zakaran damben duniya Muhammad Ali, sun ce za a yi jana'izarsa ranar Juma'a a garin da aka haife shi, wato Louisville da ke jihar Kentucky ta Amurka.

Wani kakakin iyalansa ya ce, marigayi Muhammad Ali sananne ne a duk duniya, kuma zai so a bai wa jama'a damar halartar jana'izarsa.

Bill Clinton, tsohon shugaban Amurka yana cikin wadanda zasu gabatar da jawabin alhini a lokacin jana'izar marigayin da ya mutu yana da shekara 74.

Marigayin ne dai ya tsara yadda za a yi jana'izarsa, bisa tanadin addininsa na musulunci.

Obama ya yi alhini:
Hakkin mallakar hoto whitehouse.gov

Shugaba Obama ya kira mai ɗakin marigayin ta waya, inda ya yi ta'aziyya da bayyana alhinin rashin Muhammad Ali.

Obama ya ce, yadda jama'a a duk duniya ke alhinin rashin Muhammad Ali ya nuna cewa, ya yi rayuwa abar misali.

Kafin nan dai an yi addu'oi ga marigayin a mahaifarsa Louisville.

Magajin garin birnin Greg Fischer ya ce, marigayi Muhammad Ali ya yi amfani da ɗaukakarsa wajen yaɗa sakon nuna ƙauna da neman zaman lafiya a duniya.

Muhammad Ali dai ya rasu ne ranar Juma'a a wani asibitin Arizona.