Rayuwar Muhammad Ali 1942 - 2016

Latsa wannan domin sabunta bayanai
Hakkin mallakar hoto AFP

Barkanmu da ziyartar shafin BBC Hausa kai tsaye domin samun cikakkun bayanai kan fitaccen dan damben nan na duniya, Muhammad Ali wanda Allah ya yi wa rasuwa. Sai ku kasance da mu.

1:15Ed Picson, shugaban hukumar dambe ta Philippines ya ce Ali fitaccen dan dambe ne wanda duniya ba za ta taba mantawa da shi ba.

Hakkin mallakar hoto Getty

12:59 Dan damben Birtaniya, Anthony Josua, ta shafinsa na Instagram ya ce Muhammad Ali ne ya zaburar da masu dambe kamarsa a duniya.

Hakkin mallakar hoto Getty

12:55George Foreman, mutumin da MUhammad Ali ya doke a gasar 'Rumble in the Jungle' a Kinshasha, ya bayyana Ali a matsayin mutum na musamman.

Hakkin mallakar hoto AFP

12:30 Firaiministan Ingila, David Cameron, ta shafinsa na Twitter, ya bayyana marigayi Ali da gwarzo a harkar dambe sannan kuma mai nuna jarumta wajen nemawa mutane hakki.

Hakkin mallakar hoto AP
Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Muhammad Ali tare da jama'a a Khabul

12:26 Tony Bellew wanda shi ma wani jarumi ne a duniyar wasan dambe, ya bayyana Muhammad Ali da jan gwarzo a sana'ar dambe.

Hakkin mallakar hoto Getty

12:21Gary Lineker, tsohon dan wasan kwallon kafar Ingila wanda kuma yake sharhi kan wasan na kwallon kafa, ya ce idan dai ana batun dambe ne aka yi maganar Ali, to sai a rufe batun.

Hakkin mallakar hoto Getty

12:17 Shahararren dan damben nan ajin masu nauyi, Mike Tyson ya bayyana rasuwar Muhammad Ali da babban rashi a duniyar dambe, ta shafinsa na Twitter.

Hakkin mallakar hoto EPA

12:11 Yanzu haka dai mutane na ta bayyana alhininsu dangane da mutuwar Muhammad Ali, daga ko'ina a fadin duniya.

Hakkin mallakar hoto AFP

12:07 Daya daga cikin 'ya'yan Muhammad Ali, Laila Ali, ta gaji mahaifin nata wajen sana'ar dambe, kuma ita ma ta shahara.

Hakkin mallakar hoto Other

11:44 Ya kuma auri mata hudu a rayuwarsa.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ali tare da daya daga cikin matan da ya aura

11:41 Muhammad Ali ya rasu ya bar 'ya'ya guda takwas.

Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Daya daga cikin 'ya'yan Ali mata, Laila Ali ta rungume mahaifinta

11:36 Ya kuma zabi ya yi amfani da sunan bawansa mai suna Muhammad Ali.

Hakkin mallakar hoto Getty

11:35 Cassius Clay ya sauya sunansa zuwa Muhammad Ali, bayan da ya karbi musulunci.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ali a tsakiyar musulman Amurka

11:30 Sunansa na asali shi ne Cassius Mercellus Clay

Hakkin mallakar hoto Getty

11:29 Yaya aka yi wannan jarumi ya samo suna Muhammad Ali?

11:25 A haka, yana rawar hannu ya kunna wutar bude gasar Olympics ta Atlanta da aka yi a 1996.

Hakkin mallakar hoto Getty

11:23 Bayan wasan da suka yi ne da Frazier cutar kyarma ta same shi.

Hakkin mallakar hoto Kevin C. Cox Getty Images
Hakkin mallakar hoto AP

11:20 Sai dai kuma Ali bai ji dadin fafatawar da ya yi da Joe Frazier ba.

11:17 Ya kuma lashe gasar ta dembe sau 56 a fafatawa 61 da ya yi a duniya.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Hakkin mallakar hoto Getty

11:14 Muhammad Ali ya yi ritaya daga dambe a 1981.

Hakkin mallakar hoto PA

11:13 Kisan da ya yi wa George Foreman ne ya ba wa Muhammad Ali damar lashe gasar 'Rumble in the Jungle'.

Hakkin mallakar hoto AP

11:10 A 1974, ya sanya zare da kakkarfan dan demben nan, George Foreman, a Kinshasha, Zaire. A lokacin, kowa ya mika wuya cewa Foreman ne zai kasa Ali, amma Ali sai gashi Ali ya kai Foreman kasa.

Hakkin mallakar hoto AFP
Hakkin mallakar hoto AP

11:08 Muhammad Ali ya shaidawa duniya cewa shi ne dan damben da ya fi kowanne, kuma ba a samu wanda ya tanka masa ba. Ya kasance dan damben da ya gagara.

Hakkin mallakar hoto Getty

11:05 Shi ne dan dambe na farko da ya kafa tarihi na lashe gasar ta dambe ajin masu nauyi har sau uku.

Hakkin mallakar hoto AFP
Hakkin mallakar hoto AP

11:02 Muhammad Ali dai shahararren dan dambe ne wanda tauraruwarsa ta fara haskawa a 1964, a inda ya dauki kofin farko, bayan da ya doke abokin karawarsa, Sonny Liston.

10:55 Shin wane ne Muhammad Ali? Domin samun bayani za ka iya sauraron wannan rahoto.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

10:43 Yayi ritaya daga dambe ne a shekarar 1980, amma a baya bayan nan yana fama da rashin lafiya, inda koda a farkon bara sai da ya kwanta a asibiti.

Hakkin mallakar hoto AP

10:41 Dattijon yana fama ne da cutar da ta shafi numfashi, wadda kuma cutar tsufa ta kyarma ta Ζ™ara ta'azzara ta.

Hakkin mallakar hoto Kevin C. Cox Getty Images

10:39 Kafin nan dai ya kwanta a asibiti a jihar Arizona dake Amurka. Ya rasu yana da shekaru 74.

Hakkin mallakar hoto Getty

10:37 Fitaccen zakaran damben duniya da ya kafa tarihi, Muhammad Ali ya rasu.