Nigeria: 'An kwato biliyoyi daga barayin gwamnati'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Buhari ya sha alwashin kwato kudade da kadarorin gwamnati.

Ministan yada labarai na Najeriya, Lai Muhammad, ya ce gwamnatin Buhari ta kwato fiye da Naira biliyan 78, kwatankwacin dala miliyan 185 daga hannun wadanda suka wawure kudaden kasa.

A wata sanarwa da ofishin ministan ya fitar, ma'aikatu daban-daban ne suka samu zarafin kwato kudaden daga ranar 29 ga Mayu 2015 zuwa 25 ga Mayu 2016.

Sanarwa ta kara da cewa ana sa ran dawo da kudade daga kasashen ketare da yawansu ya kai dala miliyan 321.

Bugu da kari, sanarwar ta ce an kwato filaye da gonaki da gidaje da motoci da kuma jiragen ruwa guda 239.

Wannan sanarwa dai tana zuwa ne mako guda, bayan ranar da shugaba Buhari ya ce zai bayyana kudaden da aka kwato daga hannun barayin gwamnati, ta wuce.

Shugaban dai ya yi alkawarin yin hakan ne ranar da gwamnatinsa ta cika shekara guda cif-cif a kan karaga.

Rashin bayyana kudade da kadarorin kuma ya janyo kace-nace a kasar.

Hakkin mallakar hoto NGR
Image caption Buhari tare da ministocinsa

Jadawalin yadda aka karbo kudaden da kadarori ta hannun ma'aikatu:

 • Kudade lakadan da EFCC ta karbo: Naira 39,169,911,023.00
 • Kudaden haraji da aka biya ta asusun bankin JP Morgan: Naira 4,642,958,711.48
 • Ofishin mai ba wa shugaban kasa shawara kan tsaro: Naira 5,665,305,527.41
 • Harajin kaya da ofishin mai ba wa shugaban kasa ya karbo daga hannun kamfanoni: Naira 529,588,293.47
 • Kudaden da ke asusun EFCC na babban bankin kasa CBN wadanda ta kwato: Naira 19,267,730,359.36
 • Kudaden haraji da hukumar ICPC ta karbo amma suna asusunta da ke bankin CBN: Naira 869,957,444.89
 • Kudaden da ofishin ministan shari'a ya karbo: Naira 5,500,000,000
 • Kudaden da hukumar ICPC ta karbo: Naira 2,632,196,271.71
 • Kudaden da hukumar tsaro ta farin kaya ta kwato: Naira 47,707,000.5

Kudaden da ake sa ran karbowa daga kasashen waje:

 • Switzerland: $321000000
 • Birtaniya: £6900000
 • Hadaddiyar Daular Larabawa: $310501
 • Amurka : $6225.1

Akai kuma kudade da kadarori da har yanzu ba'a kammala magana ba wajen kwato su wadanda suka hada da kudaden da ke bankuna da sunkai Naira biliyan 8, da dala biliyan daya da miliyan 800

Haka zalika, akwai kudaden da aka rike a Bankuna Naira biliyan 48 da miliyan 281, da Dala biliyan 7 da miliyan 131.