Kwarewar Muhammad Ali a duniyar dambe

Hakkin mallakar hoto PA

An haifi fitaccen dan damben nan Muhammad Ali ranar 17 ga Janairun 1942, a Louisville na jihar Kentucky da ke Amurka.

Muhammad Ali dai ya zamo kamar magori mai wasa kansa da kansa, inda yake yi wa kan nasa kirari iri-iri.

Sunansa na ainihi shi ne Cassius Clay, amma bayan da ya shiga musulunci sai ya sauya suna zuwa Muhammad Ali.

Ya shiga musulunci ne a shekarar 1964 bayan ya lashe kambun zakaran damben duniya.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Muhammad Ali a lokacin ziyararsa zuwa Kabul

Muhammad Ali dai ya ƙi shiga yaƙin Vietnam, matakin da ya sa aka janye kambun zakaran damben duniya da yake da shi.

Marigayin dai ya lashe dukkan dambe 56 daga cikin 61 da ya taɓa karawa.

Sai dai kuma a 1984, shekaru 4 bayan ya yi ritaya daga dambe an gano yana fama da cutar ƙyarma, wadda kuma ta shafi iya maganarsa da kuma motsa sassan jikinsa.

Muhammad Ali ya yi fice wajen yaƙi da nuna bambancin launin fata da kare marasa karfi.