Shark ya hallaka wata mace a Australia

Wani katon kifi Shark ya hallaka wata 'yar Australia a gabar tekun kasar, kuma wannan shi ne karo na biyu da hadari irin hakan ke faruwa kasa da mako guda.

'Yan sanda sun ce ta na ninkaya ne a cikin teku da ke kusa da birnin Perth na kasar a lokacin da kifin ya kai mata hari.

Masun ta da suka isa wurin dan aikin ceto, sun ce kifin ya fi girman kwale-kwalen da suke ciki mai girma mita biyar da rabi.

A ranar juma'a wani mutum da kifin ya kai wa hari ya rasu, kwanaki uku da aukuwar lamarin. Daga bisani ne hukumomi suka kama wani katon kifin Shark fari, da suke kyautata zaton shi ne ya kai wa mutumin hari.

Wakilin BBC a Australia ya ce sabon harin na yanzu zai diga ayar tambaya a zukatan jama'a ta yadda hukumomi ke tafiyar da lamarin.

Image caption Ana gargadin masu nin kaya su kula da hadarin Shark a teku.