Buhari ya isa London domin ganin likita

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa birnin London domin neman maganin ciwon kunnen da yake fama da shi.

Shugaban ya tashi ne daga filin jirgin saman Abuja ta jirgin saman shugaban kasa mallakar rundunar sojin kasar mai lamba 5N FGT da misali karfe 10:10 na safe agogon kasar.

"Akwai mutumin da ba ya ciwo ne?", Shugaban ya tambaya lokacin da manema labarai suka tambaye shi sakon da zai aike wa 'yan kasar domin kwantar musu da hankali.

Tun farko dai fadar shugaban ta ce Buhari zai je London din ne bisa shawarar likitocinsa wadanda suka dauki kwanaki suna faman yi masa maganin cutar amma abin ya faskara.

Sharhi: Jimeh Saleh, Editan-riko na BBC Hausa

Image caption Shugaba Buhari ya ce kowa na iya yin rashin lafiya

Kafofin watsa labaran Najeriya ne suka fara bayar da labarin ciwon kunnen Shugaba Muhammadu Buhari a watan jiya bayan ya soke ziyarar da yake shirin kai wa birnin Lagos.

Sai dai sa'o'i kadan bayan fitar da labaran, wani mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar da sanarwa, inda ya ce lafiyar shugaban, mai shekara 73, lau, yana mai karawa da cewa bai je Lagos ba ne saboda ayyuka sun yi masa yawa.

Sai dai an fara nuna damuwa kan koshin lafiya shugaban kasar bayan ya soke ziyarar da zai kai yankin Niger Delta a makon jiya.

Fadar shugaban kasar dai ta yi gum da bakinta tun daga lokacin sai jiya ta tabbatar cewa shugaban ba shi lafiya.

Mutane da dama na ganin ya kamata fadar shugaban kasar ta fara ba da labarin rashin lafiyar tasa, ba wai 'yan kasar su ji labarin daga kafafen watsa labarai ba.