MURIC ta yi tir da kisan Bridget a Kano

Kungiyar MURIC mai kare hakkokin Musulmi a Najeriya, ta yi Allah-wadai da kisan gillar da wani gungun mutane ya yi wa wata Kirista a birnin Kano na arewacin kasar, sakamakon zarginta da yin batanci ga Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.

A wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta MURIC ta kira wannan hukunci da mutanen suka yanke a matsayin wani wuce-gona-da-iri da ya kaucewa karantarwar addinin Musulunci.

Ta kara da cewa ko da a ce an kama matar dumu-dumu da wannan laifi, kamata ya yi a kai ta gaban hukuma, domin Musulunci bai yarda da daukar doka a hannu ba.

A don haka kungiyar ta yi kira ga hukumar 'yan sanda da ta bi diddigin maganar don zakulo wadanda suka aikata kisan tare da hukunta su kamar yadda doka ta tanada.

Sanarwar ta kuma ce, "A cikin surah ta 59 aya ta 4 a Al-kur'ani an umarci dukkan Musulmai su yi biyayya ga mahukunta da kuma dokar kasa. Kowa zai iya samun kansa cikin irin wannan barna da zauna-gari-banza suka aikata don haka gara tun wuri mu yi wa tufkar hanci."

MURIC ta ce Musulunci yana girmama mata, don haka bai yarda da cin zarafinsu ba ta kowacce fuska.

Ko a ranar Asabar ma, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da wannan al'amari da ya faru, inda ya mika sakon ta'aziyarsa ga iyalan matar.

Ya kuma yi umarni ga hukumomin tsaro da su tabbatar da an hukunta wadanda suka aikata hakan.

A ranar Juma'a ne wasu mutane suka kashe matar mai suna Brigdet Agbawe, bisa zarginta da yin batanci ga Manzon Allah mai tsira da aminci a kasuwar Kofar Wambai da ke birnin na Kano.