An soma azumin watan Ramadan

A Najeriya, an soma azumin watan Ramadan bayan mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubukar, ya bayyana ganin wata ranar Lahadi.

A wata sanarwa ga al'ummar Musulmi, Sa'ad Abubakar, ya bukaci 'yan kasar su yi wa shugabanni addu'a:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Hukumomin Saudiyya ma sun bayyana cewa ganin watan na Ramadam, inda su ma suka soma azumin.

Jami'a a Qatar, da Dubai da wasu kasashen yankin Gulf su ma sun yi irin wannan sanarwa.

Hakan ta faru ne bayan an bayyana ganin watan Ramadan.

Ramadan dai wata ne mai alfarma ga musulmi, domin kuwa a cikinsa ne aka saukar da Al Ƙur'ani mai tsarki.