Haɓaka sassan ɗan adam a jikin alade

Image caption Wasu na ganin za a sabawa dokokin kare martabar kowacce halitta.

Masana kimiyya a Amurka suna ƙoƙarin shawo kan matsalar ƙarancin muhimman sassan jikin ɗan adam da ake buƙata domin yi wa masu larura dashe.

Masanan dai suna so ne su haɓaka wasu sassan jikin ɗan adam a cikin alade ta hanyar amfani da wata dabarar kimiyya da ke sauya fasalin ƙwayoyin halitta.

Binciken, wanda ake yi a jami'ar California da ke Davis, ya ƙunshi yin allurar ƙwayoyin halitta da za su iya hayayyafa ga ɗan tayin alade, wanda kuma zai haifar da abin da zai yi aiki a jikin ɗan adam.

Sai dai kuma wannan aiki yana cike da cece-kuce, inda wasu suke ganin zai iya saɓawa ƙa'idojin kare martabar kowacce halitta.