Ra'ayoyin 'yan Nigeria kan kudin da aka kwato

Hakkin mallakar hoto
Image caption Biliyoyin naira aka kwato daga hannun tsoffin jami'an gwamnati

Gwamnatin Najeriya ta bayyana yawan kuɗaɗe da kadarorin da ta ƙwato ya zuwa yanzu daga wasu jami'an gwamnatin da ta shuɗe.

Wata sanarwa daga ofishin ministan yada labaran kasar Lai Mohammed, ta ce kudaden zasu kai kusan dala biliyan 10.

A cewar sanarwar, ma'aikatu daban-daban ne suka samu zarafin kwato kudaden daga ranar 29 ga Mayu 2015 zuwa 25 ga Mayu 2016.

Wasu 'yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu kan wadannan kudade da aka karɓo:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti