Wadanne shugabannin Afirka ne suka tafi jinya a waje?

Gawar Levy Mwanawasa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Mwanawasa ya mutu bayan ya yi fama da shanyewar barin-jiki sau biyu

Labarin da aka bayar cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi birnin London domin neman maganin ciwon kunne ba sabon abu ne ga shugabannin kasashen Afirka ba.

Shugabannin kasashen Afirka da dama sun fita kasashen waje neman magani, wasun su ma sun mutu a can.

A shekarar 2010 Shugaba Umaru Musa 'Yar Adua ya mutu bayan ya dawo daga Jamus inda ya je neman magani.

A shekarar 2012, shugaban kasar Guinea-Bissau Malam Bacai Sanha ya mutu a wani asibitin Faransa.

Jaridar Mail and Guardian ta Afirka ta kudu ta yi wa Zambia shagube saboda shugabannin kasar biyu ne suka mutu a kasashen waje.

Shugaba Levy Mwanawasa ya mutu a Faransa a shekarar 2008, yayin da Shugaba Michael Sata ya mutu a Birtaniya a shekarar 2014.

Shi ma shugaba mai-ci Edgar Lungu ya je kasashen waje a shekarar 2015 domin neman maganin ciwon makogwaro.

Shugaban Algeria Abdelaziz Bouteflika ya shafe kusan watanni uku a Faransa yana karbar magani bayan ya yi fama da shanyewar barin-jikinsa a shekarar 2013.

Shekara uku bayan haka ne kuma ya kwashe kwana biyar yana karabar magani a Switzerland.

A kwanan baya, jaridar News Day ta Zimbabwe ta bayar da labarin cewa Shugaba Robert Mugabe yana Singapore, inda suka ce a can ne yake yawaita yin jinya.