Akwai hadari fitar Burtaniya daga Tarayyar Turai- Yellen

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugabar Bankin Amurka, Janet Yellen

Shugabar Bankin Amurka, Janet Yellen ta yi gargadi Burtaniya cewa idan ta yi karambanin fita daga cikin kungiyar tarayyar Turai za ta gani kwaryar shanta ta fuskar tattalin arziki.

Ta ce taku daya da ka iya sauya tunanin masu zuba-jari shi ne kuri'ar raba-gardamar da za a kada a Burtaniya. Idan aka goyi bayan fitar Burtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai, to, wasu manyan abubuwa da suka shafi tattalin arziki za su biyo baya.

Da take fayyace wa Amurkawa sarkakiyar da ke tattare da ficewar Burtaniya daga kungiyar tarayyar Turan, Shugabar Asusun ajiyar kudaden wajen Amurka ta bayyana cewa hankali masu zuba jari zai karkata zuwa wani wuri daban idan Burtaniya ta goyi bayan fita daga kungiyar.

Tuni dai Sakataren Baitulmalin Amurka da Hukumar ba da lamuni na duniya da kuma Bankin Ingila suka gargadi Burtaniya cewa babu alheri a cikin fita daga kungiyar tarayyar Turan, amma masu goyon bayan fitar Birtaniyar sun yi watsi da wannan gargadin.