Burundi: 'Yan sanda sun kama dalibai

Jamian tsaro a kasar Burundi
Image caption Jamian tsaro a kasar Burundi

'Yan sanda a Burundi sun tsare wasu dalibai kan zargin bata hotunan shugaba Pierre Nkurunziza.

Ana tuhumar daliban da rubuta kalaman batanci ga shugaban kasa wanda laifi ne da ake yanke wa hukuncin shekara goma a gidan kaso.

Mazauna birnin Bujumbura sun ce, mutane biyu suka samu raunuka a ranar juma'ar da ta gabata lokacin da 'yan sanda suka bude wuta akan dalibai da ke zanga zanga.

Daruruwan dalibai wadanda shekarun wasu daga cikinsu ya kai goma sha biyu suka yi zanga zanga domin maida martani kan matakin sai dai sun ce yan sanda sun bude masu wuta.

A watan daya gabata aka kori dalibai sama da dari uku daga wata makaranta a garin Ruziba bayan da ma'aikatan makarantar suka gano wasu litatafai da aka bata hotunnan shugaba Nkurunziza wadanda kuma aka rubuta kalaman batanci a ciki.

Sai dai asusun kula da yara na duniya ya yi Alla wadai kan kamen da kuma daliban da aka kora kuma ya ce ya kamata a rika mutunta makarantu a matsayin wurin da yara zasu iya karatu ba tare da wata matsala ba.