'Hillary ce za ta yi wa Democrat takara'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hillary Clinton ta ce akwai sauran aiki a gabanta

An ba da labarin cewa Hillary Clinton ta samu adadin kuri'un da ake nema ta lashe zaben fidda-gwanin dantakar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Democrat.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya ce ta samu kuri'a 2,383, wato adadin kuri'un da ake nema kafin a lashe takarar fidda-gwanin.

Nasarar da ta samu a Puerto Rico da kuma kuri'un da ta samu a karshe daga manyan wakilan jam'iyyar ne suka taimaka mata wajen lashe zaben.

Da wannan nasarar Hillary Clinton za ta kasance mace ta farko da ta zama 'yan takarar babbar jam'iyyar siyasa irin Democrat a Amurka.