Bama-bamai sun fashe a birnin Santabul

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An ce abun ya fashe ne a daidai lokacin da wata motar safa dauke da 'yan sanda ke wucewa ta kusa da wurin.

Hukumomi sun ce akalla mutum 11 ne suka mutu bayan wani abu ya fashe a tsakiyar birnin Santanbul na kasar Turkiyya ranar Talata da safe.

An kuma ce abun ya fashe ne a daidai lokacin da wata motar safa dauke da 'yan sanda ke wucewa ta kusa da a lardin Vezneciler.

Tuni dai motocin daukar majinyata suka isa wurin.

Babu wata kungiyar da ta dauki alhakin tayar da bama-baman.

Ana yawaita kai hare-hare a kasar ta Turkiyya a baya bayan nan sakamakon tayar da jijiyar wuyan da Kurdawa 'yan a-ware ke yi da kuma rikicin da ake yi a makwabciyar kasar, Syria.