Buhari na tuhuma ta da rashawa - Jonathan

Shugaba Buhari da Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A watan Mayun bara ne Jonathan ya mika mulki ga Buhari

Tsohon Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bincike shi kan zargin aikata cin hanci da rashawa.

Mista Jonathan ya shaida wa gidan talabijin na Bloomberg cewa, "tabbas sun bincikeni, hakika an bincike ni."

Sai dai ya ki bayyana abinda binciken ya bankado, yana mai cewa yano so ya bar gwamnatin Shugaba Buhari ta yi aikinta.

Shugaba Buhari ya zargi tsaffin jami'an gwamnatin Mista Jonathan da satar biliyoyin daloli, zargin da Jonathan ya musanta tare da kare gwamnatinsa.

"Mun yi matukar kokari wurin rage cin hanci da rashawa," a cewar Mista Jonathan, wanda ya shugabanci Nigeria daga shekara ta 2010 zuwa 2015.

Mista Jonathan ya kuma musanta zargin da shugaba Buhari ya yi cewa ya bar masa "lalitar gwamnati babu komai" lokacin da ya bar mulki a shekarar 2015.

Ya kara da cewa, "Babu yadda za a yi ace ya gaji lalitar gwamnati babu komai a ciki. Ba zai yiwu ba".

A watan Mayun 2015 ne Shugaba Buahari ya maye gurbin Mista Jonathan, inda ya zamo shugaba mai ci da ya sha kaye a zabe a karon farko a tarihin Nigeria.