An kai hari sansani 'yan hijira a Jordan

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jami'an leken asiri uku sun mutu a harin

Gwamnatin Jordan ta ce mutane biyar ne suka mutu sakamakon harin da aka kai ofishin leken asiri da ke sansanin 'yan gudun hijirar Palasdinawa mafi girma a kasar.

Wani mai magana da yawun gwamnatin ya ce cikin wadanda suka mutu har da jami'an leken asiri uku a sansanin na Baqaa da ke kusa da babban birnin kasar Amman.

Ya bayyana hakan a matsayin wani aikin ta'addanci.

Ba a cika samun irin wadannan hare-hare a kasar Jordan ba.

Har yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.