Gawar Muhammad Ali ta isa garinsu

Muhammad Ali Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Asabar ne Muhammad Ali ya rasu

Gawar marigayi zakaran damben duniya Muhammad Ali, ta isa garin da aka haife shi wato Louisville, da ke jihar Kentucky a Amurka, yayin da ake ci gaba da shirin yin jana'izarsa a ranar Juma'a.

Jerin gwanon motoci ne ya ɗauko gawar Muhammad Ali daga filin jirgin sama na Louisville.

Wakilin BBC ya ce, ''Iyalan marigayi Muhammad Ali sun ce, suna bin umarninsa da ya bayar shekaru da dama da suka gabata cewa, idan ya mutu yana son a binne shi a garin da ya girma.

Marigayi Muhammad Ali dai ya na cikin shararrun mutane da suka haska a fagen wasanni cikin ƙarni na 20.

Muhammad Ali ya mutu ranar Asabar sakamakon cutar kyarma.