IS 'ta kai hari' kan sojojin Nigeria

Hakkin mallakar hoto none
Image caption Cibiyar kungiyar IS yana kasashen Syria da Iraki

Kungiyar IS reshen Yammacin Afrika wadda aka fi sani da Boko Haram, ta yi ikirarin kai wani hari a kan dakarun Najeriya a Jihar Yobe da ke yankin arewa maso gabashin kasar.

An fitar da wannan ikirarin ne ta wata manhajar aikewa da sakonni ta Telegram ta kungiyar IS din.

Sanarwar ta ce sojojin daular sun kai hari a kan ofishin 'yan sanda da barikin soji a Kanama da ke yankin Yunusari, ta kara da cewa mutane bakwai aka kashe, sannan sun kwace makamai da yawa a harin.

Sai dai babu cikakken bayani kan lokacin da aka kai harin.

Hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kai wa a Najeriya sun ragu sosai sakamakon kokarin sojojin kasar da na hadin gwiwa suke yi na ganin sun murkusheta.

A watan Maris din shekarar da ta gabata ne kungiyar Boko Haram ta yi mubaya'a ga kungiyar IS.

A kalla mutane 20,000 ne suka rasa rayukansu sannan miliyoyi suka rasa muhallansu sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram.