An yi kuskuren kama Medhanie

Hakkin mallakar hoto NCAPOLIZIA DI STATO
Image caption Mutumin da ake zargi da fataucin 'yan cirani

Abokan dan kasar Eritriyar nan da 'yan sanda suka tisa-keyarsa daga Sudan zuwa Italiya, bisa zarginsa da fataucin 'yan ci-rani, sun ce an yi kuskuren kama shi, saboda ba mai laifi ba ne.

Masu shigar da kara a Italiya sun ce Mered Medhanie shi ne Madugun masu fataucin 'yan ci-rani daga yankin Afirka ta tsakiya da Libiya zuwa Turai, inda suke amfani da jiragen ruwan da lafiya ba ta ishe su ba, tare da yi musu kazamin lodi.

Da suka ga hotunan mutumin da aka kama da sunan Mered Medhanie, bayan an garzaya da shi Italiya, abokansa sun ce sam ba wanda jami'an tsaron ke nema ba ne, hasali ma abokin nasu da aka kama shi ma dan ci rani ne, kuma salihin mutum.

Haka kuma wakilin BBC ya ce ko da hotunan mutum biyu aka duba za a ga cewa wanda ake neman ya fi abokin nasu tsufa.

Sai dai ya zuwa yanzu hukumomi a Birtaniya da Italiya ba su ce komai kan lamarin