Yaron da kishiya ta kakkarya ya samu tallafi

Hakkin mallakar hoto Aisha buhari
Image caption Labarin Musa ya ja hanakalin 'yan Najeriya sosai inda aka rika wallafa hotunansa a shafukan sada zumunta

Mai dakin shugaban kasar Najeriya, Hajiya Aisha Buhari ta ziyarci Musa, yaron da ake zargin matar baban sa ta azabtar a wani asibiti da ke Abuja.

Rahotanni dai na cewa matar ta kakkarya yaron ne, wanda ke hannunta bayan da mahaifinsa ya saki mahaifiyarsa, a jihar Kano da ke arewacin kasar.

Lamarin ya ja hankalin 'yan kasar sosai, inda aka rika wallafa hotunansa a shafukan sada zumunta da muhawara.

Aisha Buhari ta ambato likitoci na cewa Musa zai samu sauki sai dai abin takaicin shi ne ba zai taba komawa kamar yadda yake a baya ba, tana mai cewa zai yi fama da wasu matsalolin har tsawon rayuwarsa.

Aisha Buhari ta bukaci gwamnatin jihar Kano da ta tabbatar cewa an hukunta wadanda su aikata wannan laifin.

Makonni biyu da suka gabata ne dai 'yan sandar jihar Kano suka kama Zainab da Hafsatu Musa, wadanda ake zargin su ne suka karairaya kafafuwa da kuma hannayen Musa mai shekara biyu.