Stephen Keshi ya mutu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Keshi ya horas da kungiyoyin kwallon kafar Togo da Mali

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta ce tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasar wanda kuma shi ne tsohon kocin Super Eagles, Stephen Okechukwu Keshi, ya rasu.

Hukumar, wadda ta bayyana haka a shafinta na Twiter, ta ce Mista Keshi ya rasu ne da tsakar daren ranar Talata a birnin Benin da jihar Edo.

Ba ta bayyana abin da ya yi ajalinsa ba, sai dai rahotanni na cewa ya mutu ne sakamakon bugun zuciya.

Marigayin da kuma Mahmoud El Gohary na kasar Masar su ne 'yan wasa biyu kadai da suka yi nasarar daukar kofin gasar CAF ta Afrika a matsayin 'yan wasa da kuma koci.

Keshi ya horas da kungiyoyin kwallon kafar Togo da Mali, kana ya zauna a kulob din Anderlecht na kasar Belgium.