Shirin samar wa matasa aiki a Najeriya

Hakkin mallakar hoto NYSC
Image caption Wasu matasa da suka kamala shirin bautan kasa

Gwamnatin Najeriya ta ce a farkon makon gobe za ta kaddamar da shirinta na samar da ayyukan sa-kai na koyarwa 500,000 ga 'yan kasar wadanda suka kammala karatun jami'a amma ba su da aiki.

A karkashin tsarin dai za a rika biyan wadannan matasa albashi yayin da suke aikin koyarwa kafin su samu aiki.

Wannan shiri dai daya ne daga cikin shirye-shiryen da gwamnatin Najeriyar ta yi alkawarin aiwatarwa don inganta rayuwar al'umma kai-tsaye.

Wata sanarwa da ta fito daga ofisihin mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo, ta ce a ranar Lahadin makon gobe ake sa ran shafin intanet din da duk mai sha'awa zai je don cike bukatarsa zai fara aiki, ko da yake tun ranar Asabar za a bude shafin wanda adireshinsa shi ne npower.gov.ng.

Sanarwar ta kara da cewa yayin da suke wannan aikin sa-kai na karantarwa a makarantun firamare da na sakandare, za a rika biyan matasan naira 23,000 duk wata .

A jawabin da ya yi na cika shekara guda da hawansa mulki ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da kaddamar da shirin, wanda ya ce an ware kudin da ake bukata don aiwatar da shi a kasafin kudin kasar na bana.

Masu suka dai sun jima suna zargin gwamnatin da gazawa wajen daukar matakan da suka dace don farfado da tattalin arzikin kasar, da samar da ayyukan yi.