Ba za mu tattauna da Buhari ba - Avengers

Image caption Kungiyar Niger Delta Avengers ta hare-hare da dama a yankin

Kungiyar Niger Delta Avengers (NDA), ta ce ta yi watsi da bukatar gwamnatin Nigeria na yin tattaunawar sulhu da ita domin kawo karshen hare-haren da ta ke kai wa kan bututan mai.

NDA ta kuma ce ta kai hari kan wata rijiyar mai mallakar kamfanin Chevron da ke yankin na Niger Delta a ranar Laraba.

A ranar Talata ne ministan mai na Najeriya ya ce gwamanti za ta fara tattaunawa da tsagerun yankin na Naija Delta ciki har da NDA.

Sai dai kungiyar ta wallafa a shafinta na twitter cewa: "ba za mu yi wata yarjejeniya da wani kwamiti ba".

Ta kara da cewa sai dai gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi "tattaunawar sulhun ita kadai".

Hare-haren da kungiyar ke kai wa kan bututan mai da na iskar Gas a yankin ya sa adaddin man da kasar ke hakowa ya yi raguwar da bai taba yi ba a shekaru 20.

Wannan ya sa farashin mai ya tashi a kasuwannin duniya, yayin da kuma kudaden shigar da kasar ke samu ya ragu.