An daure ma'aikacin banki saboda sata

Ma'aikacin banki Hakkin mallakar hoto EFCC
Image caption Olawale Garuba ya amsa laifinsa

Wata kotu a birnin Lagos na Nigeria ta yanke hukuncin daurin shekaru 39 ga wani ma'aikacin banki da ya sace kudin wani kostoma da ya rasu.

An sami Olawale Garuba da laifin hada baki da wasu mutane domin sace naira miliyan 30 daga asusun marigayin wanda ke hulda da bankin da ya ke aiki.

Babbar kotun jihar Lagos ta same shi da laifuka 13 inda aka yanke masa hukuncin shekaru uku a gidan yari a kan kowanne - sai dai zai yi su ne a lokaci guda.

Jami'an bankin ne suka mika shi ga Hukumar Yaki da Yiwa tattalin Arzikin Kasa Ta'annati (EFCC), inda ta gurfanar da shi a gaban kuliya a shekarar da ta gaba ta.

Da farko Garuba ya musanta tuhumar da aka yi masa, amma daga baya ya amsa laifinsa, abin da ya sa aka hanzarta shari'ar.

Mai shari'a Oluwatoyin Ipaye ta babbar kotun jihar Lagos ta ce mutumin ya nuna cin amanar da bankin ya ba shi, tare da jefa marayu cikin wahala.

A don haka ta yi watsi da bukatar lauyansa na yi masa sassauci a hukuncin da ta yanke masa.

Ta ce son zuciya ne ya fi karfinsa inda ya kai shi ga rasa aikinsa wanda dubban jama'a ke fafutukar ganin sun samu.