Bill Gates ya faɗi sirrin kiwon kaji

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Bill Gates ya ce zai aiwatar da shirin ne a kasashen da ke shiyyar Afirka ta yamma.

Attajirin Ba'Amurken nan, Bill Gates ya ce yana shirin taimaka wa al'umomin da ke kasashe marasa galihu da dubban kaji da nufin bunkasa kiwonsu.

Ya yi amanna da cewa kiwon kajin zai taimaka wajen inganta rayuwar jama'a, tare da rage talauci, musamman ga mata wadanda za su yi dawainiyar kiwon su.

Attajirin ya ce akwai sirri sosai a harkar kiwon kaji, saboda za su dinga hayayyafa suna ninka yawansu.

Mr Bill Gates ya ce zai aiwatar da shirin ne a kasashen da ke shiyyar Afirka ta yamma.

A cewarsa, binciken da ya gudanar ya nuna cewa a duk lokacin da aka raya 'yan tsaki goma, to sukan yi albarkar da ta kai dala 10,000 a duk shekara.